Old school Swatch Watches
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na talatin da takwas


Sayyed Zakzaky2

Ko ya halasta ga mace ta nemi mijinta ya sake ta?

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ina hukuncin ruwan da aka zuba a roba don yin wankan janaba, alhali a wajen wankan, ruwan na komawa cikin na robar?

Daga Husain Muhammad D. Almajirai Tsakuwa Dawakin Kudu jihar Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To ai ba inda aka ce ruwan da ka yi wanka da shi ba zai yiwu ka sake yin wanka da shi ba. Bilhasali ma in robar babba ce, yana iya shiga cikin robar ma ya yi wankansa na janaba din. In ma ya fito, in ma akwai wadansu da za su yi wankan duk suna iya shisshiga, duk ma su yi ta yin wankan da shi. Wato ruwan da aka wanke janaba da shi, shi bai zama najasa ba ballantana ya hana a sake yin wani wankan janaba da shi. Ruwan da aka wanke bayan gida ne da shi, wato ka kama ruwa ka wanke bayan gida, shi ne wannan ba zai yiwu a yi mafani da shi wajen yin alwala ko wanka ba. Amma ba wanda ya wanke jikinsa don da janaba, sai kuma ruwan ya zama ya najastu ba. Lalle yana nan da tsarkinsa.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, menene hukuncin cin naman gafiya, bushiya, damo, kurege, guza da sauran ire-irensu?

Daga Husain Muhammad D. Almajirai Tsakuwa Dawakin Kudu jihar Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To, duk haramun ne. Ba makaruhi ba kamar yadda ya shahara a wajen amawa. Wai har suna cewa wai karahiyya, to lalle ya wuce nan. In ma karhanci ne, sai mu ce karhancin haramci ne. Haka zalika kuma duk nau'o'in beraye gaba daya, har da beran Misra da zomo, duk cin su haramun ne. Haka kuma duk abin da ke jan ciki, wanda ya hada da dangin su damo da guza, wanda ya hada har da su kadangare da kado da ma duk wani abu mai jan ciki, har da macizai, duk sun haramta a ci.

TAMBAYA: Akramakallah, na yi sammako don zuwa wani gari tun kafin lokacin sallar asubahi, don haka ne kawai zai sa na riski abin da ya kai ni. To kafin na karasa garin, sai rana ta fito. Shin zan yi salla a mota ne ko zan bari sai na sauka?

Daga Husain Muhammad D. Almajirai Tsakuwa Dawakin Kudu jihar Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Mai tambayar ga dukkan alamu ya jahilci lokacin salla, tun da ya dauka cewa ana yin sallar subahi ne in rana ta fito. To in alfijir ne ya keto ake yin sallar subahi. Saboda haka in ya fita gida kafin ketowar alfijir, to bayan ketowar alfijir kafin gari ya dan wattsake daidai gwargwadon abin da aka dauka lokacin sallar subahi ne, lokacin da ya fi kyau a yi, wanda a ibarar ama takan ce masa mukhtari, to mu kuma mukan ce masa lokacin Fadila. To lalle a wannan lokacin zai sauko daga motar ne ya yi sallarsa. In kuma har ma bai sauko ba, to yana da lokaci har ya zuwa wattsakewa mabayyani, kafin ketowar rana, dole ya sauko ya yi salla. In kuwa har ya bari rana ta fito, to ya yi laifi, ya aikata haramun, ya bar wajibi. Saboda haka yanzu ramuwa ta kama shi, amma kuma ya yi zunubi mai yawa.

TAMBAYA: Akramakallahu. Yaya zan yi da cin nama idan na sami kaina a Ingila ko Amerika?

Daga Muhammad M.Mustafa Kano.

SHAIKH ZAKZAKY: To, Alhamdu lillahi, ina jin shi wannan bai je Ingila ko Amerikan bane. In ya je zai ga ba shi da wata matsala da nama, insha Allahu. Saboda akwai musulmi a wadannan wuraren, kuma akwai nama na halas. Har ma akwai kantunan da ake sayar da naman halal. Za ka ga ma an rubuta HALAL balo-balo, har ma a gidajen cin abinci ma akwai na halal. Saboda haka in dai batun nama ne, ba shi da mishkila a yanzu duniyar nan da mike ciki a kasashe, saboda ko'ina akwai musulmi. Sai dai in ba wajen musulmi bane, wanda suka tabbatar masa da halascinsa, to ba zai ci naman ba kenan sam-sam, ko ma abin da ya fito daga naman.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ya taba yin bayani kan karin gashi ga 'ya mace, saboda haka nake neman karin bayani?

Daga Muhammad M. Mustafa Kano.

SHAIKH ZAKZAKY: Tunda na taba yin bayani, saboda haka insha Allahu wancan bayanin ma, ai sai ya je ya duba da kyau. Wala'alla abin sani shi ne, wannan dai halas ne. Ba kamar yadda ama take cewa shi ne 'wasila walmustausila ba'. Domin "wasila wal mustausila" yana da wata ma'ana, wanda yake shi ne sahihi, cewa ita ce Kawaliya, wadda take sadar da mazinaci da mazinaciya. To wasila ita ce wannan Kawaliya din, mustausila kuwa, ita ce wadda aka sada ta da mazinacin, ba wai mai sada gashi ba. Kuma shi sada gashi ba wani abin da aka ruwaito dangane da shi. Ba a ruwaito haramcinsa ba. Saboda haka ya halatta tunda ba a sami haramcinsa ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Menene hukuncin sahu, kuma ta ina ake farawa?

SHAIKH ZAKZAKY: Abin sani dangane da yin sallar jam'i shi ne, idan mutane da yawa suka hadu zai kasance ana yin sahu-sahu ne, sahun farko sannan na biyu sannan mabi da su, kuma ya zama akwai tazara da ke tsakaninsu bai wuce abin da zai wadatar ta yadda ba wani nisa tsakanin kan wanda ya yi sujuda, da kafar Liman, in yana bayan Liman ne. Haka kuma tsakanin kan na sahu na biyu da kafar na sahun farko da sauransu. Sauran bayani in ya duba cikin littafin fikihu zai gani. Kuma wannan ko shakka babu ya nuna maka cewa ta gaba ake fara sahu, ba ta baya ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Na ji ana cewa tasirin mummunan aikin da iyaye suka yi yana bin 'ya'yansu, kamar idan uba ya zama mazinaci, to sai an sami 'ya'yansa sun zama mazinata. To shin idan haka ne wadannan 'ya'yan suna da laifin yin zina kenan duk da cewa kamar gado suka yi? To kuma in ya tuba ya bari fa?

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle da gaske ne mummunan aiki na iyaye yana tasiri a kan 'ya'yansu kamar yadda kyawawan ayyuka na iyaye kuma yana tasiri a kan aikin 'ya'yansu. To amma ladan aikata aiki mai kyau yana ga wanda ya aikata, har da kuma wanda ya shiryatar da shi ga yi din. Kamar yadda kuma wanda ya yi laifi yana nan ga wanda ya aikata laifin har da kuma wanda ya nuna a yi, ba tare da an tankware laifin na wanda ya yin a karshe ba. Alal misali, idan laifin Uba ya sa yaronsa ma ya zama mai laifi, to dan yana da zunubin laifinsa, kuma Uban yana da zunubin wanda ya aikata da kuma na yaron, ba kuma na yaron ne aka dauko aka sa masa ba. Kamar yadda kuma haka yake a wajen lada. Saboda haka mutanen kirki akan sami haka nan ya bi su, kuma lalle kowa yana da lada na aikinasa ne ko zunubin aikinasa. To kuma kamar yadda ka ce, in ya tuba ya bari fa? To ai shi kenan wanda ya tuba, Allah yana son masu tuba. Allah (T) mai karbar tuba ne.

TAMBAYA: Mutum ne mai yawan tafiye-tafiye don neman abin masarufi, kuma tafiyar da ta kai misalin kasaru, amma kuma ba ya da cikakkiyar sana'a ko aikin yi, sai dai 'yan buge-buge. To menene hukuncinsa dangane da yin salla da azumi?

Daga Muhammad Abubakar Funtuwa jihar Katsina.

SHAIKH ZAKZAKY: To lalle tunda yana tafiya ne don neman abin masarufi, saboda haka tafiya ce ta halas matukar abin da zai aikata na nema na abin masarufin na halas ne. Da misali zai yi niyyar cewa zai je wani gari, amma in ya je zai yi sata ne, to ka ga wannan za a ce tafiyar ta zama ta haram. Amma za shi ne in ya sami wani aiki zai yi ya sami lada, a biya shi ladan, to ka ga da ma tafiyar ta zama ta halas kenan. Saboda haka matukar ta kai 'masafa,' nisan a yi kasaru, to zai kasarta salla, kuma zai sha azumi.

TAMBAYA: Ko ya halasta ga wanda yake bin mazhabar Ja'afariyya ya ki yin Basmala a salla saboda takiyya?

Daga Umar Sani Jihar Barno.

SHAIKH ZAKZAKY: To lalle ban san inda zai bukatu ga yin takiyya na barin yin basmala ba. Saboda ko ba komai yanzu haka dai ita basmala an san ta, a nan tsakankanin mutanenmu akwai wadanda suke yi, misalin 'yan Tijjaniyya suna yin basmala, bi ga mazhabar Shafi'iyya, wanda ya ce ana bayyana basmala. Sannan kuma sauran wurare ma wadanda yake ba su bayyana basmala din, suna yin ta a boye, mutum zai ji sun fada, amma ba su bayyana jauharin murya ba. Saboda haka in dai dangane da basmala ne, in ma ta kai ma shi in ya bayyana wani zai ga wani abu ne daban, to ai yana iya asirtawa, amma ba dai ya bari gaba daya ba. Kuma ni wannan ban dai san ta inda zai zama muhallin takiyya ba. Amma dai ya rage masa, saboda ita takiyya da ma ba ta da ka'ida. Ka'idarta shi ne kai ne yadda ka sami kanka ka san abin da ka gain, kuma kai ne kake sama wa kanka mafita.

TAMBAYA: Shin ya halasta ga mace ta nemi mijinta ya sake ta saboda ta ga yana tauye mata hakkinta na aure da suka zama wajibi?

Daga Muhammad N. Ibrahim Malumfashi.

SHAIKH ZAKZAKY: Abin dai da yake ladabi shi ne ya zamana ta kai shi inda za a sasanta ne, ta kai shi kara masalan, ko in da za a sasanta su. In a nan ne ta ce ita kawai ba ta da bukatar auren ne, ta sami haka nan. Amma ba ita da shi ta ce masa ya sake ta ba.

TAMBAYA: Shin da gaske ne akwai karyar da aka yi wa mutum rangwamen ta?

Daga Muhammad N Ibrahim Malumfashi.

SHAIKH ZAKZAKY: To,idan misali mutum ya zo da bindiga yana neman Muhammadu N. Ibarahim ya kashe, kuma bai san shi ba, sai ya gan ka ya ce ko kai ne Muhammad N. Ibarahim? To za ka yi gaskiya ne ka ce kai ne Muhammad N. Ibrahim? Wato akwai muhallin da idan mutum ya zama ya fadi abin da shi ne gaskiya, amma sai ya zama sanadiyyar da aka zalunci wani, ko aka cuci wani, to lalle shi laifi ya yi ba gaskiya ba. Kamar misali wani azzalumi na neaman wani talaka ya kashe, ko ya kwace masa hakki, ya ce ina yake? Kai kuma ka san inda yake, za ka ce ba ka sani ba. Ko kuma ina ya boye dukiyar? In ka san inda ya boye, ba za ka ce ai ga ta nan ba, a matsayin kai mai gaskiya ne ba. In kuwa har ka fada, to lalle akwai hukunci a kanka. Saboda a nan ba sunan abin da ka yi gaskiya bane, sunan sa wauta.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din